Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sardar Reza Talaei-Nik, mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro da daukin Sojojin, a yammacin Juma'a, ranar 4 ga watan Ordibehesht (daidai da 24 ga Afrilu), a cikin wata hirar labarai ta musamman, bayan ya girmama tunawa da shahidai, ya bayyana cewa:
"A matsayina, ina girmama tunawa da jagoranmu mai girma, shahidi, Ayatullahil-Uzma Imam Khamene'i (Allah ya jiƙansa), haka nan ina tunawa da dukkan kwamandoji, dukkan mayaƙa, da kuma al'ummar da suka yi shahada a wannan babban yakin Ramadan, suka kuma sami wannan babbar falala - daga yaran Minab zuwa dukkan fararen hula".
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ya kara da cewa: "A cikin sa'o'in farko na wannan yakin da aka tilasta mana na uku, a taron Majalisar Tsaro, gungun kwamandojin Hédkwatar Sojoji da dakarun Pasdaran (IRGC), da abokan aiki a Majalisar Tsaro sun sami shahada. Sannan jami'an 'yan sanda abokan aiki da suka kasance a wurin a wannan taron".
Shahadar Manajoji 6 Na Ma'aikatar Tsaro Tare Da Amir Nasirzadeh
Sardar Talaei-Nik ya ci gaba: "Amir Laftana-Janar Dr. Nasirzadeh, Ministan Tsaro, tare da mataimakan ministoci biyu na Ma'aikatar Tsaro sun halarci wannan taron sun kuma sami shahada. Baya ga Ministan Tsaro, Shahid Sardar Laftana-Janar Dr. Mozafarinia, mataimakin ilimi na Ma'aikatar Tsaro, da kuma Sardar Laftana-Janar Dr. Jabal Ameliyan, mataimaki kuma mai taimakawa fannin bincike na Ma'aikatar Tsaro, tare da wasu manajoji hudu na Ma'aikatar Tsaro su ma sun sami shahada".
Ya kara da cewa: "A yakin Ramadan, wasu daga cikin abokan aiki da iyalansu su ma sun hadu da ayarin shahidai, muna girmama dukkan wadannan 'yan uwanmu da iyalansu shahidai".
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ya ci gaba: "Ina roƙon Allah ya kara daukakak da lafiya ga jagoranmu mai girma, magajin nagartaccen Imam, shahidi Ayatullah Sayyid Mujtaba Husayni Khamene'i (Allah ya kara masa lafiya), babban kwamandan sojoji, da dukkan al'ummar Iran, da mayaƙan da suka yi cikin jarumta da dakewa da ƙarfi da jajircewa, har suka kai ga sanya abokan gaba su mika wuya a wannan fagen karawar".
Nasarori 7 Da Aka Tabbatar Da Su Da Kuma Nasarori 3 Da Ba Su Cika Tabbatar Da Su Ba Na Al'ummar Iran A Tilastaccen Yaki Na Uku
Sardar Talaei-Nik, a ci gaba da bayanin yanayin yakin na uku "Babban Yakin Ramadan", ya ce: "Kwanaki 55 ke nan da fara tilastaccen yaki na uku da babban yakin Ramadan; kwanaki 40 muna fuskantar yakin soji kai tsaye da abokan gaba na Amurka da Sahayoniya, kuma kusan kwanaki 15 muna cikin yanayin tsagaita wuta."
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ya bayyana: "Yanayin yakin yana nuna cewa al'ummar Iran da mayaƙa sun samu nasarori bakwai na asali, haka nan akwai nasarori uku da suke gab da tabbatuwa, wadanda dole ne a ci gaba da su don kammala nasarorin".
Da yake nuni da nasarorin bakwai, ya kara da cewa: "Nasarar farko ita ce nasarar soji. Abokan gaba sun shiga yakin da nufin ruguza ƙarfin makamai masu linzami da soji na Iran, amma a wannan burin na su sun gaza gaba daya. Sojojin suna da ikon sararin samaniyar ƙasashen mamaya har zuwa lokacin tsagaita wuta, kuma har yanzu ba a yi amfani da wani gagarumin sashi na damar makamai masu linzami ba".
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ya ci gaba: "Duk da samuwar wasu raunin farko a fannin tsaron sararin samaniya, amma sai da aka lalata tsaron abokan gaba da sauri da yawa. Dukkan sansanonin Amurka a yankin sun fuskanci ruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuki na Iran, wannan ya nuna cewa ƙarfin kai hare-haren na kasar ba wai ya lalace ba, kai sai dai ma ma ya kara ƙarfafuwa ne".
Sardar Talaei-Nik ya lura: "Wannan damar ta samo asali ne daga tanadin sama da shekaru 25 na shiri da saka hannun jari a fannin makamai masu linzami da Ma'aikatar Tsaro, Sojoji, kamfanoni masu zaman kansu, da kamfanonin ilimi da fasaha suka yi, kuma a yau masu lura da al'amuran duniya sun tabbatar da fifikon makamai masu linzami na Iran".
Ya ce nasara ta biyu ita ce nasarar siyasa: "Duk da shahadar da aka yi wa jagoranmu mai girma Jagora Imam (Khamene'i) da wasu kwamandoji a kwanakin farko na yakin, tsarin Jamhuriyar Musulunci ba wai kawai bai rushe ba, sai dai ma ya kara zama na al'umma, ya karfafu, kuma ya fi ƙarfi fiye da da".
Sardar Talaei-Nik ya ce nasara ta uku ita ce nasarar yanki: "Abokan gaba suna neman wargaza Iran kuma sun tsara kungiyoyin 'yan aware, wadanda a cewar Donald Trump, ya ba su makamai da kudi, amma wannan aikin ya gaza saboda tsarin dabara na hukumar leken asiri da tsaro, wanda ya kai ga kiyaye iyakokin kasar".
Ya ce nasara ta hudu ita ce ta zamantakewa: "Yawan halartar jama'a a fagen daga, har bayan tsagaita wuta, wani abin al'ajabi ne na zamantakewa; yadda sama da mutane miliyan 30 suka yi rajista a gangamin 'Janfada' (sadaukar da kai), wanda ba shi da misali a duniya na taron jama'a kamar haka".
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ya ce nasara ta biyar ita ce ta tsaro: "Abokan gaba suna neman haifar da hargitsi da rashin tsaro a cikin kasar, amma saboda kaifin hankali da basirar jama'a da kokarin jami'an 'yan sanda, dakarun Basij, da hukumomin tsaro, kasar tana cikin yanayi na tsaro, kwanciyar hankali, da haɗin kai".
Ya ce nasara ta shida ita ce ta geopolitical: "An sanya mashigar Hormuz a ƙarƙashin kulawar tsaro da ƙarfin Iran kuma ya zama makamin sarrafawa don cimma burin bukatun al'ummar Iran; ta ya zamo yadda sojojin abokan gaba a Tekun Oman sau da yawa suka ja da baya saboda tsauraran martanin sojojin Iran".
Sardar Talaei-Nik ya ce nasara ta bakwai ita ce samar da goyon bayan kasa da kasa: "Yunkurin abokan gaba na kulla kawancen adawa da Iran ya ci tura, a maimakon haka, an samu guguwar ra’ayoyin masu adawa ga Amurka da Sahayoniya a duniya; ciki har da zanga-zangar da aka yi a Amurka kan manufofin yaki na gwamnatin wannan kasar".
Nasarori 3 Da A Kai Ga Tabbatar Da Su Ba Na Al'ummar Iran
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro a ci gaba ya yi nuni da nasarori uku da suka kusa kammaluwa: "Na farko, batun diyya da rama hasarar al'ummar Iran, wanda za a bi ta hanyoyi daban-daban akan abokan gaba da sauran kasashe".
Ya kara da cewa: "Na biyu, hukuntawa da daukar fansa ga shahidan al'ummar Iran, wannan tsari har yanzu bai kammala ba gaba daya, ana kuma bibiyar yiwuwar hakan".
Sardar Talaei-Nik ya ce manufa ta uku ita ce dakile barazanar nan gaba: "Dole ne mu kai ga matakin hanawa (daƙilewa) wanda zai iya dakile duk wata barazanar da za ta iya zuwa kan tsaron kasa a nan gaba".
Ya jaddada: "Yanayin yakin yana nuna cewa al'ummar Iran tana tura abokan gaba zuwa ga kammala sarkar mika wuya, kuma a halin yanzu muna kan matakin kusa da cimma wadannan manufofi."
Abubuwan Da Suka Jagoranci Nasarar Sojoji A Talastaccen Yaki Na Uku
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro a ci gaba da bayyana abubuwan da suka sa sojoji suka yi nasara a wannan yakin, ya ce: "Abin da ya sanya sojoji su kasance masu ƙarfi, nasara, da iko a wannan yakin da kuma fagen da suka gabata, shi ne jagoranci da gudanarwa da farko; jagorancin Ubangiji, da ikon Allah, da da kokarin jagororin da aka sanya, da kuma shirye-shiryen da aka yi a Hédkwatar Khatamul-Anbiya (SAW) da kwamandojin Soji, Pasdaran, 'Yan sanda (Faraja), da tsarin komutocin da aka tsara, tare da basira da shiri na sarrafa dukkan tsare-tsare".
Ya kara da cewa: "Abu na biyu, shi ne ruhin imani, jarumtaka, da jajircewa na mayaƙa; ruhin da ya bayyana a fagen yaƙi da ƙarfi da jajircewa, kuma duk da shahadar kwamandoji, ya kara karfafa kuzari da ƙarfin sauran sojoji, domin a al'adun Musulunci da tsakanin al'ummar Iran, shahada tana sake haifar da ƙarfi ne".
Sardar Talaei-Nik ya ci gaba: "Abu na uku, kayan aiki da makamai ne. Tare da ƙarfin mutane da na ruhaniya, makamai ma suna da tasiri".
Samar Da Makamai Sama Da Nau'i 1,000 A Jamhuriyar Musulunci Iran
Ya ci gaba: "A yau, sama da nau'in makamai dubu (1,000), da suka hada da makamai masu linzami, jirage marasa matuki, na'urori, da kayan aiki daban-daban, an samar da su gaba daya ta hanyar gida, bisa ilimi da fasaha, kuma na Iran ne, ta hannun sojoji, Ma'aikatar Tsaro, kamfanoni masu zaman kansu, da kamfanonin ilimi da fasaha".
Ya bayyana: "Wannan damar sakamakon saka hannun jari sama da shekaru 25 a masana'antar tsaro; yadda ko da an lalata wasu cibiyoyi, ana ci gaba da samarwa da tallafawa a fadin kasar, a bayyane da kuma a boye. A wannan hanya, kusan kamfanoni 9,000 suna aiki tare da sojoji da Ma'aikatar Tsaro".
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ya yi ishara da cewa: "A fannin kai daukin kota kwana, baya ga ajiyar dabaru, a lokacin yaki ana samar da kayan gyara, kayan asali, da ababen da ke karkashin nau’rorin tsaro, ana samar da su, kuma ana ba kai daukin fasaha da ilimi ta hanyar tura masana da kwararru ga mayaƙa".
A karshe ya jaddada: "Fagen yakin sojoji da fagen halartar jama'a sune manyan fage biyu na nasara, wadanda suke samun tallafawa da fage hudu; wadanda suka hada da fagen gwamnati da bayar da ayyuka, fagen kafafen yada labarai da yaki ruwan sanyi, shigar jama'a, da fagen diflomasiyya – wadanda gaba daya ke jagorantar kasar zuwa ga babbar nasara".
---
Your Comment